Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin a Nijeriya ya kai ziyara a jihar Taraba
2020-02-07 10:15:14        cri

 

Daga ranar 5 zuwa ranar 6 ga wata, jakadan kasar Sin dake kasar Nijeriya Zhou Pingjian ya kai ziyarar aiki jihar Taraba dake arewa maso gabashin kasar, inda ya gana da mataimakin gwamnan jihar Haruna Manu da kai ziyara ga ma'aikatan kamfanonin Sin.

 

 

A yayin dake ganawa da Haruna Manu, Zhou Pingjian ya yi bayani kan yadda kasar Sin take yaki da cutar numfashi, ya kuma kara da cewa, a bana ake cika shekaru 20 da kafa dandalin tattauna hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, kuma kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da Nijeriya a fannonin ma'amala tsakanin jami'an bangarorin biyu, da kiwon lafiya da dai sauransu.

 

 

A nasa bangare, malam Haruna Manu, ya ce Nijeirya tana yabawa matuka da yadda kasar Sin take aikin yaki da cutar numfashi cikin kwanciyar hankali, kuma kasarsa tana goyon bayan kasar Sin wajen yaki da cutar. Ya kara da cewa, gwamnati da al'ummomin Nijeriya, suna girmamawa da goyon bayan dukkanin al'ummomin kasar Sin wajen hana yaduwar cutar, ya kuma yi fatan alheri ga jama'ar kasar Sin wajen cimma nasarar wannan yaki cikin sauri. Bugu da kari, ya ce, jihar Taraba tana da albarkatun ruwa da gonaki, tana kuma maraba da zuwan kamfanonin kasar Sin don su zuba jari. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China