Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe mutane 26 a wani hari a tsakiyar Najeriya
2020-02-04 11:01:52        cri
Wani jami'in dan sandan jihar Plateau ya bayyana jiya Litinin cewar, kimanin mutane 26 aka kashe a harin baya bayan nan da aka kai a jihar dake shiyyar tsakiyar Najeriya.

Hukumar 'yan sandan jihar ta bayar da sanarwa, inda aka tabbatar da cewa, sama da gidaje 190 aka lalata a sanadiyyar hare-haren wanda wasu mahara da ba'a san ko su wanene ba suka kaddamar a kananan hukumomi biyu dake jahar tsakanin 26 zuwa 28 ga watan Janairu.

Sanarwar ta ce, an raunata wasu mutanen da dama a sanadiyyar hare-haren, kuma akwai al'ummomin wasu kauyuka kimanin biyar a kananan hukumomin Bokkos da Mangu dake fuskantar munanan hare hare a cikin 'yan kwanakin nan.

Sanarwar ta kuma ce, a hare haren, an kashe mutane 14 a Kwatas, mutane 4 a Sabon Barki, mutum guda a yankin Changet, sai kuma mutane 7 da aka kashe a yankin Marish.

Ya zuwa yanzu, an kama mutane 11 da ake zargin suna da hannu wajen shirya hare haren, kuma ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin, in ji sanarwar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China