Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba a samu bullar cutar numfashi a Nijeriya ba, in ji cibiyar NCDC
2020-02-03 11:18:48        cri

Rahotanni daga cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Nijeriya wato NCDC, sun musanta jita jitar cewa wai an gano masu dauke da cutar numfashi a kasar.

A jiya Lahadi, cibiyar ta sanar a birnin Abuja, fadar mulkin Nijeriya cewa, ta riga ta kafa wani dakin gwaji, domin yin nazari kan samfurorin da ta samu daga jikunan da aka yi zaton na masu dauke da cutar ne, amma sakamakon binciken cibiyar ya nuna cewa, ba a gano ko mutum guda dake dauke da cutar ba. Sa'an nan kuma, cibiyar NCDC ta yi kira ga al'ummomin Nijeriya, da kada su saurari, kuma yada jita-jita.

Ta kuma ba da shawarar cewa, ya kamata dukkanin Sinawa da suka isa kasar cikin kwanaki 14 da suka gabata, su gabatar da yanayin lafiyar su ga cibiyar ta NCDC. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China