Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban AU ya jaddada aniyar Afrika na neman tsakaita bude wuta a Libya ba tare da sharadi ba
2020-01-21 10:21:26        cri
Shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika (AU), Moussa Faki Mahamat, ya bayyana matsayar Afrika na cikakken goyon bayan tsakaita bude wuta a Libya ba tare da gindaya wasu sharruda ba da kuma mutunta aniyar MDD na sanya takunkumin hana shigar da makamai kasar mai fama da tashin hankali.

Shugaban kungiyar mai mambobin kasashen Afrika 55, a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, ya jaddada muhimmancin aiwatar da cikakken shirin tsakaita bude wuta a Libya ba tare da gindaya wasu sharruda ba, da mutunta takunkumin da MDD ta sanya na hana safarar makamai a kasar, da kuma daukar kwararan matakan hukunta dukkan wadanda suka saba yarjejeniyar.

Mahamat ya kara nanata muhimmancin hadin kan dukkan bangarorin Libya da bin hanyoyin tattaunawar siyasa wanda ya kunshi sanya ido don warware takaddamar, AU ta fitar da wannan sanarwar ne a ranar Litinin bayan kammala babban taron kasashen duniya game da batun rikicin Libya wanda aka gudanar a birnin Berlin, na kasar Jamus ranar Lahadi.

Jami'in gudanarwar na hukumar AU ya sake jaddada matsayin kungiyar ta kasashen Afrika game da batun Libya a bayyane, yana mai cewa babu wani matakin soji da zai iya warware dambarwar siyasar kasar, kuma duk wani matakin da za'a dauka tilas ne ya shafi matakan siyasa wanda kasar Libyan zata jagoranta don tattaunawar sulhu. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China