Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka kamu da cutar numfashi a Sin ya kai 2,744 kana ta hallaka mutane 80
2020-01-27 15:48:38        cri
Hukumomin lafiya a kasar Sin, sun tabbatar da kamuwar mutane 2,744 da cutar nan ta numfashi, wadda kwayoyin cutar coronavirus ke haddasawa, sun kuma ce kawo yanzu cutar ta hallaka mutane 80. Mahukuntan sun ce ya zuwa daren jiya Lahadi, cikin wadanda ke dauke da cutar a halin yanzu, akwai mutane 461 dake cikin mawuyacin hali.

A ranar ta Lahadi, yawan sabbin wadanda aka tabbatar cutar ta kama sun kai mutum 769, akwai kuma mutane 3,806 da ba a kai ga tabbatar da ko sun kamu da cutar ba tukuna. Kaza lika adadin wadanda suka rasu a ranar sun kai mutum 24. Har ila yau akwai mutane 51 da suka warke, bayan samun kulawar jami'an lafiya.

Hukumar lafiya ta kasar Sin ta ce jimilar wadanda ake kokarin tantancewa sun kai 5,794. Cikin wannan adadi, jimillar wadanda suka yi cudanya ta kusa da masu dauke da cutar ya kai 32,799. Cikin wannan adadi akwai mutane 583 da bayan tantance su an sallame su, yayin da likitoci ke ci gaba da tantance wasu mutanen su 30,453.

A wajen babban yankin kasar Sin kuwa, adadin wadanda suka kamu da cutar a Hong Kong ya kai mutum 8, da mutane 4 a Taiwan, da kuma mutane 5 a Macao.

A kasashen waje kuwa, an samu bullar cutar a Thailand mai mutane 7, da Japan mai mutane 3, da Koriya ta kudu mai mutane 3, da Amurka mai mutane 3. Sauran sun hada da Vietnam mai mutum 2, da Singapore mai mutane 4, da Malaysia mai mutane 3, da Nepal mai mutum 1, da Faransa mai mutane 3, da kuma Australia mai mutane 4. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China