2020-01-05 15:58:42 cri |
Babban jami'i mai kula da kamfanin na CSCEC dake Masar, ya bayyana cewa ginin sabon yankin hukumar gudanarwar babban birnin kasar da ake gudanarwa a halin yanzu, babban cigaba ne ga shirin bunkasuwa da kuma zamanantar da kasar Masar, ya ce aikin gina babbar cibiyar kasuwanci birnin wato (CBD), wanda kamfanin CSCEC ke gudanarwa yana da cikin muhimman ayyukan babban birnin kasar, in ji Chang Weicai, janar manajan CSCEC a Masar, ya bayyana a yayin zantawarsa ta kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Chang ya yi wannan tsokaci ne bayan wata liyafar da ya shirya wa firaiministan kasar Masar Mostafa Madbouly, da jakadan kasar Sin a Masar Liao Liqiang a yankin da ake gudanar da aikin dogon ginin mai hawa 20. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China