2020-01-12 17:24:34 cri |
A sanarwar da ta fitar, rundunar ta ce, muddin dai gwamnati ta amince da tsagaita bude wuta, lalle su ma zasu tsagaita bude wutar, sai dai idan an karya yarjejeniyar, zasu mayar da martani mai tsanani.
Rundunar mai sansani a gabashin kasar Libya ta fara daukar matakan soja a ciki da kewayen birnin Tripoli ne a farkon watan Afrilu, a kokarin karbe iko da birnin da kuma hambarar da gwamnatin kasar dake samun goyon bayan MDD.
Dubban mutane sun mutu da kuma jin raunuka sakamakon fadan da aka gwabza, a yayin da mutane sama da dubu 120 rikicin ya raba da muhallansu.
A wata sabuwa kuma, a yau Lahadi, wasu sa'o'i bayan da rundunar ta sanar da daina daukar matakan soja, gwamnatin Libya ta amince da tsagaita bude wuta tun daga daren wannan rana. (Lubabatu)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China