Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samar da cikakkun gidajen kwana masu inganci a jihar Xinjiang a karshen shekarar 2019
2020-01-09 15:27:34        cri

Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, ta gabatar da rahoton gwamnatin jihar na shekarar 2020, inda aka nuna cewa, a cikin shekarar da ta gabata, jihar ta mai da hankali kwarai kan kawar da talauci, kuma an kebe kudin Sin har RMB Yuan sama da biliyan 37 domin wannan aiki.

A cikin wannan shekara kuma, jihar na yi iyakacin kokarin cike gibinta na karancin gidajen kwana masu inganci, da kuma kyautata gidaje marasa inganci, matakin da ya sa matalauta 9355 suka samu gidaje masu inganci, hakan ya kuma kawo karshen kwana cikin gidaje marasa inganci a jihar, ban da wannan kuma, jihar ta gaggauta samar da ruwan sha mai tsabta, matakin da ya amfana wa matalauta fiye da dubu 346.

A cikin shekarar 2020 kuwa, jihar za ta yi kokari don cimma nasarar fitar da mutane dubu 165 daga kangin talauci, da kawar da kauyuka dake fama da talauci har 560, da kubutar da gundumomi 10 daga kangin talauci, ta yadda za a tabbatar da kawar da talauci kwata kwata bisa ma'auni na halin yanzu a dukkan kauyukan jihar, domin ba da tabbaci ga jihar na shiga yanayin zaman al'umma mai matsakaicin karfi, kamar sauran yankunan kasar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China