Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban AU ya yi maraba da yarjejeniyar tsakaita bude wutar Libya
2020-01-14 11:09:35        cri
Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika (AU), Moussa Faki Mahamat, ya yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta baya bayan nan tsakanin bangarorin dake yaki da juna a kasar Libya.

Shugaban kungiyar mai mambobi kasashen Afrika 55, ya bayyana cikin wata sanarwar da aka fitar ranar Litinin, ya yi kira ga bangarori masu rikici da juna da su bayar da damar shigar da kayayyakin jin kan al'umma musamman a yankunan Tarik al-Sidra, Tarik al-Shok da Salahaddin dake birnin Tripoli.

Mahamat ya sake yin kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen ci gaba da aiwatar da shirin wanzar da zaman lafiya a kasar.

Haka zalika ya kara jaddada cewa AU, tana shirin gudanar da taron babban kwamitin AU game da batun rikicin Libya nan gaba cikin wannan watan a Brazzaville, babban birnin kasar Kongo, domin nazarin yadda za'a yi hadin gwiwa tsakanin bangarorin kananan hukumomi, shiyyoyi da kuma masu ruwa da tsaki na kasa da kasa da nufin daukar matakan kawo karshen rikicin Libya da samar da dawwamammen zaman lafiyar kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China