Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yi alwashin daidaita alamurra a Somaliya duk da yawan hare-hare a kasar
2019-12-30 10:04:14        cri
Kungiyar tarayyar Afrika AU ta yi Allah wadai da harin ta'addanci wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane 79 da raunata wasu 149 a Mogadishu ranar Asabar, AU ta lashi takobin daukar matakan daidaita al'amurra a kasar ta shiyyar gabashin Afrika duk da yawaitar hare-hare da kasar ke fuskanta.

Moussa Faki Mahamat, shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika ya ce kungiyar ta Afrika ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawar da wadannan munanan laifuka na cin zarafin jama'a, ya jaddada cewa muggan laifukan da matsoratan 'yan ta'adda ke kaddamarwa ba zai taba sanyaya musu gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiyar Somaliya ba.

Mahamat ya fada cikin wata sanarwa wadda tawagar wanzar ta zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika a Somaliya wato AMISOM ta fitar cewa, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen bada goyon baya ga gwamnatin kasar Somalia, kuma aikin da AMISOM ke gudanwar a kasar Somaliya zai tabbatar da cikar burinta na 'yantar da al'ummar kasar Somaliya da samar da zaman lafiya da tsaro a kasar. (Ahmad Fagam)

 

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China