2020-01-10 13:12:15 cri |
Ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Nijer ta ce a kalla sojojin kasar 25 aka hallaka a wani hari da aka kaddamar kan sansanin sojojin dake yammacin kasar a daren Alhamis.
Harin dai ya faru ne a sansanin sojojin dake garin Chinagodrar a kan iyakar kasar ta yammacin Afrika da Mali.
Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da harin.
Ma'aikatar tsaron kasar ta ce, an kashe sama da 'yan bindigar 60 a yayin arangamar.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China