Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kashe mutane 14 dake rakiyar jami'an hukumar zaben jamhuriyar Nijar
2019-12-27 09:58:44        cri
Ma'aikatar harkokin cikin gidan jamhuriyar Nijar ta sanar a jiya cewa, wasu mahara da ba'a tantance ko su wanene ba sun kai hari kan ayarin sojoji dake yiwa jami'an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar rakiya a shiyyar yammacin kasar a ranar 25 ga watan Disamba, lamarin da yayi sanadiyyar kashe sojoji 14 dake rakiyar, sannan soja guda ya bace, amma babu wanda aka kashe daga cikin jami'an hukumar zaben.

Babu wata kungiyar da ta yi ikirarin alhakin kai harin.

A 'yan shekarun baya bayan nan, kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi da 'yan ta'adda masu alaka da kungiyar IS masu tsattsauran ra'ayi, sun sha kaddamar da hare hare a sassan yammacin Jamhuriyar Nijar dake makwabtaka da kasashen Mali da Burkina Faso, lamarin da yayi sanadiyyar hasarar rayuka masu yawa. Ko a ranar 10 ga wannan watan na Disamba kimanin sojojin Nijar 70 aka kashe kana wasu sojojin sama da 10 sun bace a wani harin da 'yan ta'adda suka kaddamar a sansanin sojojin a shiyyar yammacin jamhuriyar Nijar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China