Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya ta sanya dokar hana fita a yankin Lamu bayan wani harin ta'addanci
2020-01-10 10:26:26        cri
Gwamnatin kasar Kenya ta sanya dokar takaita zirga zirga a gundumar Lamu dake bakin teku bayan samun hare haren ta'addanci daga mayakan kungiyar al-Shabab.

Kwamandan 'yan sandan yankin Lamu, Perminius Kioi, ya ce dokar takaita zirga zirgar za ta taimakawa hukumomin tsaro wajen sanya ido, da kuma binciko bata garin da ake zargi da kaddamar da harin a tsibirin wanda hukumar UNESCO ta sanya shi cikin jerin sunayen wurara masu tarihi na duniya.

Kioi ya fadawa 'yan jaridu cewa, dokar hana fitan da gwamnatin Kenya ta sanya za ta taimakawa hukumomin tsaro dake yankin samun damar shiga yankunan cikin sauki, da sa ido, da kuma binciko hakikanin wadanda ake zargi da kaddamar muggan laifukan cikin karamin lokaci.

Matakin saka dokar hana fitar a yankin Lamu ya zo ne bayan harin da al-Shabab ta kaddamar kan sansanin dakarun kawance na kasashen Kenya da Amurka inda wani jami'in sojan Amurka guda da wasu 'yan kwangila biyu suka mutu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China