Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Kenya ta kaddamar da layin dogon dakon kaya na Nairobi-Naivasha
2019-12-18 09:57:12        cri

A jiya ne kasar Kenya ta kaddamar da hidimar layin dogon dakon kaya na zamani (SGR) da tashar sauke manyan kwantenoni(ICD) tsakanin Nairobi da Naivasha, wadanda ake saran za su zamanantar da sufurin kwantenoni zuwa lungunan kasar da ma kasashe makwabta.

Shugaba kasar Uhuru Kenyatta da mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin Wang Yong, na daga cikin manyan bakin da suka hakarci bikin kaddamar da kashi na biyu na hidimar layin dogo da tashar kan tudu dake garin Naivasha.

A jawabinsa yayin bikin shugaba Kenyatta, ya bayyana cewa, " Yau mun kaddamar da hidimar layin dogo zuwa tashar dakon kwantenoni ta Naivasha, babu wata kalma da za mu iya kwatanta ta da wannan nasara da muka samu".

A ranar 16 ga watan Oktoban wannan shekara ce, aka fara aikin layin dogon dakon kaya na Nairobi-Naivasha mai nisan kilomita 120 da aka kaddamar, wani bangare na layin dogo na zamani da kasar Sin ta gina, wanda ya hada birnin Mombasa dake gabar ruwa da Nairobi, fadar mulkin kasar ta Kenya wanda aka kaddamar a shekarar 2017.

A nasa jawabin Wang Yong, kana manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya Kenya murnar kaddamar da sabon titin dogon. Yana mai cewa, kaddamar da titin dakon kayan, wani zakaran gwajin dafi ne na tarihin gina layin dogo a Kenya da Afirka. Haka kuma wani babban ci gaba ne a fannin hadin gwiwar Sin da Kenya da alakar Sin da Afirka a fannin shawarar "ziri daya da hanya daya".(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China