Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan kudin da aka zuba ga yankin Xinjiang a bara ya kai Yuan biliyan 18.819
2020-01-08 10:59:38        cri
Rahotanni na cewa yayin taruka biyu na yankin Xinjiang na kasar Sin, an bayyana cewa larduna da birane 19 masu taimakawa yankin, sun ci gaba da maida hankali ga yankin a fannonin yaki da talauci, da kyautata zaman rayuwar jama'a a shekarar 2019, wadanda suka zuba jari ga yankin har Yuan biliyan 18.819, da taimakawa yankin ta aiwatar da ayyuka guda 1935.

Ta haka an nuna goyon baya ga yankin, wajen gudanar da ayyukan yaki da talauci, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da bunkasa tattalin arziki da sauransu.

Bisa rahoton aikin gwamnatin yankin Xinjiang da aka gabatar, yawan moriyar da aka samu a sakamakon gudummawar da aka samar ga yankin a shekarar 2019 ya karu, har yawan kudin da aka zuba ga aikin kyautata zaman rayuwar jama'a, da kuma taimakawa garuruwan dake yankin, ya kai kashi 80 cikin dari ko fiye, kana an kafa tsarin taimakawa garuruwa da kauyuka 774 na yankin, daga garuruwa da kauyuka 820 na larduna da birane masu samar da gudummawa.

An ce a shekarar nan ta 2020, yankin Xinjiang zai yi kokarin aiwatar da shirye-shiryen taimakawa yankin, tare da larduna da birane masu samar da gudummawa gare shi, don kara samun moriya da ci gaba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China