Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masar ta yi Allah wadai da matakin majalisar dokokin Turkiyya na tura dakaru zuwa Libya
2020-01-03 09:49:06        cri
A ranar Alhamis kasar Masar ta yi Allah wadai da babbar murya kan matakin da majalisar dokokin kasar Turkiyya ta dauka na amincewar gwamnatin kasar ta tura dakaru zuwa kasar Libya mai fama da tashin hankali.

Ta bayyana amincewar da majalisar dokokin Turkiyyar ta yi da cewa tamkar yin karan tsaye ne ga dokokin kasa da kasa da kudurin MDD game da batun kasar Libya.

Ta kara da cewa, matakin zai kara haifar da mummunar illa game da zaman lafiyar yankin Mediterranean, kuma Turkiyya ce za ta dauki alhakin faruwar hakan.

Rikicin ya barke ne a Libya a shekarar 2014, sakamakon yunkurin neman madafun iko tsakanin bangarorin gwamnatoci biyu: bangaren gwamnatin hadin kan kasa ta (GNA), mai samun goyon bayan MDD dake Tripoli babban birnin kasar, sai kuma bangaren da suka ayyana kansu a matsayin dakarun sojojin kasar Libya (LNA), dake arewa maso gabashin birnin Tobruk wanda Khalifa Haftar ke jagoranta.

Masar tana goyon bayan dakarun LNA na Haftar, wadanda ke kaddamar da munanan hare-hare tun daga watan Afrilu da nufin kwace ikon birnin Tripoli. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China