Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta inganta samar da inshora domin kyautata biyan bukatun al'ummarta
2019-12-31 09:46:01        cri
Majalisar gudanarwar kasar Sin, ta ce kasar za ta inganta samar da inshora ga al'umma domin samar da tallafi mai karfi ga jama'arta da suka manyanta da kuma biyan bukatun sauran al'umma na wasu nau'ikan inshorar.

Yayin taron majalisar da aka yi jiya karkashin firaministan kasar Li Keqiang, an lura cewa kasar Sin ta shiga wani yanayi na yawan wadanda suka manyanta a cikin al'ummarta, kuma adadin wadanda suka zarce shekaru 60 ya kai miliyan 250. Majalisar ta ce abu ne mai muhimmanci samar musu da albarkatun inshora da musamman za su biya bukatunsu, tare kuma da samar da inshora ga sauran rukunonin jama'a. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China