Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan kasar Sin ya jaddada bukatar daidaita matakan ba da izni a yankunan FTZ
2019-12-03 10:25:28        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira da a sa kaimi wajen ganin an yi wa yankunan cinikayya marasa shinge cikakken gyaran fuska da zai bambance tsakanin lasisin kasuwanci da iznin yin kasuwanci a wadannan yankuna, ta yadda hakan zai saukaka matakan baiwa kamfanoni izni da ma kara shiga kasuwanni.

Kafin aiwatar da wadannan gyare-gyaren, sai kamfanoni sun samu izni kafin su samu lasisin gudanar da kasuwancinsu, matakin dake daukar lokaci.

Li ya bayyana cikin umarnin da ya bayar ta kafar bidiyo game da yin gyare-gyare da aka gudanar da jiya Litinin a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin cewa, wannan mataki na da muhimmanci wajen zurfafa yin gyare-gyare a fannin daidaita harkokin mulki, raba madafun iko, inganta ka'idoji da hidimomi, gami da samar da yanayin kasuwanci da ya dace da inganta karfin kasuwa.

Don haka, ya bukaci a kara yin kokari, wajen kara kafa yanayin kasuwanci da ya dace da kasuwar kasa da kasa, bisa doka, a wani mataki na bullo da sabbin sa'na'o'i da bunkasa ci gabansu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China