Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta zartas da sanarwar shugaba game da matasa, zaman lafiya, da tsaro
2019-12-13 11:02:21        cri
A jiya Alhamis kwamitin sulhun MDD ya zartas da sanarwar shugaba game da batun matasa, zaman lafiya da tsaro, wanda ya kunshi bukatar daukar matakai don kara shigar da matasa cikin shirin tabbatar da zaman lafiya.

An amince da kudurin ne bayan muhawarar da aka gudanar a watan Oktoba, mai taken "wayar da kan matasa domin kawar da amon tashin bindiga kafin shekarar 2020," wanda ake burin kawo karshen dukkan tashe tashen hankula a Afrika zuwa shekarar 2020, muhimmin shiri ne wanda kungiyar tarayyar Afrika AU ta kaddamar da shi.

Sanarwar ta nanata cewa, a halin da ake ciki yanzu matasa su ne kaso mafi yawa na mutanen da matsalolin rikice rikicen 'yan bindiga ya fi shafa da kuma za su taka muhimmiyar rawa wajen yin riga kafi da shawo kan tashe tashen hankula.

A cikin sanarwar, kwamitin sulhun MDD ya gabatar da wasu matakai kuma ya shawarci kasashe mambobin kwamitin MDD da su kara daukar matakai don cigaba da wayar da kan matasa da nufin kawar da amon bindiga a Afrika nan da shekarar 2020.

Haka zalika sanarwar ta kara kwarin gwiwa ga mambobin kwamitin sulhun MDD don su tsara wani shiri wanda zai bayar da damammakin da za'a shigar da wakilan matasa a shirin wanzar da zaman lafiya da daukar matakan zartarwa a dukkannin mataki tare da shigar da matasa mata cikin wadannan shirye shiryen. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China