![]() |
|
2019-12-21 16:53:21 cri |
Fabien Neretse, mai shekaru 71, a ranar Juma'a an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 25, a yayin zaman kotun ta kasar Belgium na ranar Alhamis.
Ana tuhumar madugun da laifukan kisan kare dangi da aikata laifukan yaki kan tsiraru 'yan kabilar Tutsi a lokacin fadan da ya barke a kasar Rwanda na tsawon watanni uku a shekarar 1994, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da miliyan 1.
A cewar sanarwar da hukumar CNLG ta fitar, Neretse, ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa a lokacin gudanar da shara'ar, shi ne mutum na farko da aka yankewa hukunci a kasar Belgium game da laifukan kisan kare dangi.
Kotun majistiri ta kasar Belgium ta tanadi hujjoji a cikin shekaru masu yawa kan batun, tun daga lokacin da aka tsare Neretse a kasar Faransa a shekarar 2011. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China