Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'i: Hadin gwiwa da Sin karkashin fasahar Juncao yana da muhimmanci ga Rwanda
2019-12-07 15:58:21        cri
Wani jami'in ma'aikatar aikin gona ta kasar Rwanda ya ce hadin gwiwa da kasar Sin game da fasahar Juncao, wanda ake amfani da ita wajen noman lemar kwadi, da abincin dabbobi da makamashi ta hanyar tsirrai, al'amari ne mai matukar muhimmanci ga kasar Rwanda.

Patrick Karangwa, babban daraktan hukumar aikin gonar kasar Rwanda, ya ce, yin amfani da fasahar Juncao ta kasar Sin ya yi daidai da manufar shirin gwamnatin Rwanda na bunkasa aikin gona don samun kudaden shiga, ya bayyana hakan ne a lokacin bikin rufe shirin ba da horon kan fasahar.

Shirin ba da horon na tswon kwanaki 25, ya samu halartar 'yan kasar Rwanda 45 daga hukumomin gwamnati da masu zaman kansu, wanda ma'aikatar ciniki ta kasar Sin ta dauki nauyi, kana wasu kwararru daga jami'ar aikin gona da raya gandun daji ta Fujian ta kasar Sin ne suka ba da horon.

A cewar Karangwa, ana fatan shirin ba da horon zai karawa mutanen Rwanda fahimtar fasahohin aikin gona da raya cigaba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China