Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta bukaci a kara zurfafa cinikayya tsakanin kasashen Afrika
2019-12-04 10:26:20        cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta jaddada bukatar fadada harkokin kasuwanci tsakanin kasashen Afrika yayin da alkaluma suka nuna cewa kasa da kashi 20 bisa 100 na kayan da ake samarwa a Afrika ake amfani da su a cikin nahiyar.

AU ta ce Afrika tana da damammakin bunkasa harkokin cinikinta a kasuwannin cikin gida. Don haka akwai bukatar kasashen Afrika su fadada harkokin kasuwanci a tsakaninsu domin ciyar da tattalin arzikinsu gaba da kuma cin moriyar kasashen.

A bisa kididdigar da kungiyar mai mambobi kasashen Afrika 55 ta fitar ya nuna cewa, hada hadar kasuwancin dake gudana tsakanin kasashen shi ne mafi kankanta da kashi 15 bisa 100, inda kasa da kashi 20 bisa 100 na kayayyakin da ake samarwa a nahiyar ne suke yawo a tsakanin kasashen.

Sakamakon bukatar da ake da shi a halin yanzu na cike gibin kasuwanci a tsakanin kasashen Afrika, AU ta kaddamar da muhimmin taro da nufin bunkasa mu'amalar cinikayya tsakanini nahiyar, daga ranar 3-5 ga watan Disamba a helkwatar kungiyar AU dake Addis Ababa na kasar Habasha, taken taron shi ne, "Kayayyaki kirar Afrika a yi cinikinsu a Afrika." (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China