Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gibin ababen more rayuwa babban kalubale ne ga nasarar cinikayya maras shinge ta Afirka, in ji wasu kwararru
2019-07-10 10:37:52        cri
Masana a cibiyar cinikayya ta Africa50 mai helkwata a birnin Casablanca na kasar ta Morocco, sun bayyana gibin ababen more rayuwa da nahiyar Afirka ke fuskanta, a matsayin kalubale ga yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta nahiyar ko AfCFTA a takaice.

Yayin taron masu ruwa da tsaki na cibiyar, wanda ya gudana a jiya Talata a birnin Kigalin kasar Rwanda, babban jagoran cibiyar ta Africa50 Mr. Alain Ebobisse, ya bayyana yarjejeniyar ta AfCFTA, a matsayin jigon dunkulewar hada-hadar cinikayya, da ci gaban nahiyar Afirka baki daya. Ya ce ya zama wajibi nahiyar ta zakulo fasahohi masu nagarta wadanda za su ba da damar cike gibin da take fuskanta a wannan fanni.

Ita kuwa babbar jami'ar gudanarwa ta cibiyar Carole Wainaina, cewa ta yi, idan har ana son cimma nasarar aiwatar da wannan yarjejeniya ta cinikayyar Afirka, to akwai bukatar zuba jari mai gwabi a fannin samar da ababen more rayuwa a dukkanin sassan nahiyar, musamman ma fannin shimfida layin dogo, da hanyoyin mota da na sadarwa.

Cibiyar Africa50, na da abokan hulda daga kasashen Afirka 27, da bankin samar da ci gaba na Afirka, da babban bankin kasashen yammacin Afirka na BCEAO, da kuma babban bankin kasar Morocco. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China