Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara gina jami'ar ilmin sufuri ta farko a nahiyar Afirka
2019-12-03 13:51:42        cri
A jiya ne, kamfanin CCECC na kasar Sin ya fara aikin gina jami'ar ilmin sufuri ta kasar Nijeriya a jihar Katsina dake arewacin kasar Nijeriya. A jawabinsa yayin bikin fara aikin, shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin da kamfanin CCECC bisa ga gudummawar da suka samar ta gina jami'ar ilmin sufuri, jami'a ta farko a wannan fanni a nahiyar Afirka.

A matsayinta na jami'ar ilmin sufuri ta farko a kasar Nijeriya, an gina ta ne domin biyan bukatun aikin zamanintar da hanyoyin jiragen kasa na kasar Nijeriya da kamfanin CCECC yake gudanarwa. Kamfanin zai biya bukatun ma'aikatar harkokin sufuri ta kasar Nijeriya, ta hanyar gina jami'a mai inganci, tare da fara yin hadin gwiwa tare da jami'ar a wasu kwasa-kwasai don horar da kwararru a kan aikin zamanintar da hanyoyin jiragen kasa na kasar.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, jami'ar ilmin sufuri ta kasar Nijeriya za ta kasance jami'a ta farko a wannan fanni a nahiyar Afirka, wadda za ta inganta karfin fasahohi da sarrafa harkoki, da sa kaimi ga yin kirkire-kirkire kan tsarin sufuri na kasar tare da samar da karin ayyukan yi a kasar.

A nasa bangare, jakadan Sin dake kasar Nijeriya Zhou Pingjian ya bayyana cewa, kamfanonin kasar Sin kamar CCECC sun samar da gudummawa wajen inganta hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Nijeirya, kana yana fatan kasashen biyu za su kara zurfafa hadin gwiwa da sada zumunta a tsakaninsu a sabon zamani, da sa kaimi ga raya shawarar "ziri daya da hanya daya" don amfanawa jama'ar kasashen biyu. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China