Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya ba da umarni hana yin bayan gida a bainar jama'a
2019-11-21 10:27:45        cri

Jiya Laraba ne, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sanya hannu kan umarnin shugaba da nufin kawo karshen yadda jama'a ke yin bayan gida a filin Allah ta'ala nan da shekarar 2025.

Shugaba Buhari ya bukaci hukumomin tsaro, da su hada kai da gwamnati, wajen ganin an aiwatar da wannan umarni. A baya dai, shugaban ya ayyana dokar ta baci a bangaren samar da ruwan sha da tsaftar muhalli da kiwon lafiya, yana mai cewa, daukar wannan mataki zai rage yadda jama'a ke kamuwa da cututtuka da ke da alaka da ruwan sha, wadanda ke haddasa mace-mace da za a iya magancensu.

Da yake sanya hannu kan sabon umarnin shugaban, Buhari, ya kuma ba da umarnin samar da magewayai da shadda a wuraren taron jama'a, ciki har da makarantu da otel-otel da gidajen mai da wuraren Ibada da kasuwanni da asibitoci da ma ofisoshi.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China