Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an kasashen dake cikin shirin Ziri Daya da Hanya Daya sun koyi fasahohin shimfidawa da kula da layin dogo a kasar Sin
2019-08-16 13:06:49        cri
Jimilar jami'ai 35 daga kasashe 11 dake kan hanyar Ziri Daya da Hanya Daya ne suka zo kasar Sin, domin samun horo kan fasahohin shimfadawa da kula da layin dogo.

Horon na makonni 3 da ma'aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ta shirya, wanda ya gudana a biranen kasar 3 da suka hada da Chengdu, babban birnin lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin da Hefei, babban birnin lardin Anhui na gabashin kasar da kuma Shanghai.

Jami'an sun fito ne daga bangarorin sufurin jiragen kasa ko kuma na mota, na kasashen Burkina Faso da Jamhuriyar Czech da Laos da Mauritius da Mongoliya da Mozambique da Sri Lanka da Sudan da Thailand da Uganda da Vietnam. Sun kuma kammala karbar horon inda suka koma kasashensu daga birnin Shanghai a ranar Laraba.

Gerard Constant Emmanuel Guigma, daraktan bangaren fasaha na sashen kula da sufuri na kasar Burkina Faso, ya ce kasar Sin ta shawo kan yanayin muhalli masu sarkakkiya, inda ta gina hanyar sufurin jiragen kasa mai karfi, lamarin da ya ja hankalin duniya. Kuma yana fatan karin hadin gwiwa da kasar a wannan fannin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China