Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin jiragen saman kasar Afirka ta kudu ya sanar da dakatar da sufurin jiragen sa
2019-11-15 10:44:39        cri
Kamfanin zirga zirgar jiragen sama na Afirka ta kudu ko SAA a takaice, ya sanar da dakatar da dakon fasinjoji a cikin kasar, da ma masu ketarawa wasu sassan duniya. Hakan dai ya biyo bayan barazanar shiga yajin aiki ne da kungiyoyin kwadago masu aiki a fannin zirga-zirgar jiragen sama suka yi.

A ranar Laraba ne dai kungiyoyin ma'aikatan kamfanonin sarrafa karafa ta kasar, da na masu tallafawa matuka jiragen sama, suka bayyana cewa za su shiga yajin aiki, a wani mataki na neman karin albashi, da kuma turjiya ga matakin rage ma'aikata da suka ce kamfanin na SAA na shirin aiwatarwa.

Kungiyoyin sun ce za su tsunduma yajin aiki mafi girma, tun daga karfe 4 na Asubahin Juma'ar nan, wanda zai kunshi daukacin ma'aikatan dake aiki a jirage, da masu tantance fasinjoji, da masu aikin kula da na'urori.

Kamfanin SAA dai ya ce duk wani yunkuri na warware takaddama tsakaninsa da kungiyoyin kwadagon ya ci tura, don haka ya yanke kudurin dakatar da dukkanin zirga zirgar fasinjoji ta jiragensa. Ya kuma yi kira ga abokan huldarsa, da su dauki matakan sauya tikitin su zuwa wasu kamfanonin sufurin jiragen sama a lokacin tafiye-tafiye. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China