Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fadar shugaban kasar Afrika ta kudu ta kare kanta kan zargin kudaden yakin neman zabe
2019-08-11 16:08:49        cri
Kakakin shugaban kasar Afrika ta kudu Khusela Diko, ya ce shugaban kasar Cyril Ramaphosa bai aikata ba daidai ba a lokacin yakin neman zaben da ya ba shi damar darewa kan shugabancin jam'iyyar ANC mai mulkin kasar a shekarar 2017.

Kakakin ya musanta zarge-zargen da ake yadawa cewar Ramaphosa da kwamitin gangamin yakin neman zabensa sun amshi kudade daga hannun wani kamfanin kasar Bosasa, wanda aka fi sani da African Global Operations, wanda hakan ya saba dokar tsarin mulkin kasar.

A cewar Diko, tun da farko mista Ramaphosa da kwamitin yakin neman zabensa sun sha yin alkawurra cewa za su gudanar da yakin neman zabe mai tsabta, wanda ya dace da tanade tanaden dokokin kasar kuma wadanda suka yi daidai da manufofin jam'iyyar ANC mai mulkin kasar.

Wannan sanarwa tana zuwa ne bayan fitar da sakamakon rahoton kwamitin binciken da aka kafa a watan Yuli, inda shugabar kwamitin binciken korafe-korafen jama'a ta kasar Busisiwe Mkhwebane, ta zargi shugaban kasar da amsar tsabar kudi rand 500,000 na kasar, kwatankwacin dala 33,000 ba bisa ka'ida ba daga kamfani na Bosasa domin hidimar yakin neman zaben shugaban kasar a wancan lokaci. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China