2019-11-14 10:00:15 cri |
Sama da hekta 4,000 na gonaki ne ambaliyar ruwan ta lalata a garin Rann, dake karamar hukumar Kalabalge na jihar Borno, a cewar Zainab Gimba, 'yar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar yankin.
Gimba ta ce kogin Kaalia dake Kamaru ne ya tumbatsa inda ya haddasa barnar.
A cewar Gimba, daga cikin mutanen da lamarin ya fi shafa akwai dubban mata da kananan yara wadanda ambaliyar ruwan ta danawa tarko na rashin samun abinci, muhalli, da kayayyakin more rayuwa.
Mutanen suna bukatar dauki don kwashe su daga wajen, kasancewar ragowar sansanonin 'yan gudun hijirar dake kusa da su su ma suna fuskantar kalubaloli da suka hada da cunkuson jama'a ko kuma yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwan, Gimba ta tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho.
Ta bukaci a kai daukin gaggawa don dakile matsalar ambaliyar ruwan, da kuma taimakawa mutanen da lamarin ya shafa, ta ce, gaza daukar matakan da suka dace zai iya sanadiyyar salwantar rayuka masu yawa. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China