Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Najeriya ya gana da ministocin wutar lantarki da albarkatun ruwan kasar
2019-11-06 11:13:39        cri

Jiya Talata, jakadan Sin dake Najeriya Zhou Pingjian ya gana da ministan wutar lantarki Sale Mamman da ministan albarkatun ruwan kasar Suleiman Adamu, inda suka tattauna makomar hadin kan Sin da Najeriya a wadannan fannonni nan gaba.

Yayin taron wanda karamin ministan wutar lantarki Goddy Jedy Agba ya halarta, bangaren Najeriya ya nuna cewa, Sin da Najeriya na da kyakkyawan zumunci, kuma kasar tana maraba da fasahohin zamani da na'urori da kayayyaki masu inganci na kasar Sin zuwa cikin kasar, gwamnatin kasar na daukar Sin a matsayin sahihiyar kawa abin dogaro, hakan ya sa kasar take ba da muhimmanci wajen kara yin hadin kai da Sin, tare kuma da kara tuntubar juna da ingiza raya manyan ayyukan samar da wutar lantarki ta karfin ruwa don magance matsalar karancin wutar lantarki da kasar ke fama da ita, matakin da zai kasance na cin moriya tare.

A nasa bangare, jakada Zhou ya ce, bangarorin biyu sun samu ci gaba mai armashi ta fuskar hadin kai a wannan fanni, alal misali, ana gudanar da aikin tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa na Zungeru, kuma akwai makoma mai haske wajen raya shawarar "Ziri daya da hanya daya". Sin na fatan kara inganta tuntuba da Najeriya don tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma da kuma sakamakon da aka samu yayin taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika da kuma zurfafa hadin kai a dukkan fannoni.(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China