2019-11-10 15:57:24 cri |
An yi wannan kira ne yayin taron ministoci na kasashe mambobin kungiyar 55, wanda ya gudana a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.
Da take tsokaci game da wannan batu, kwamishiniyar AU mai kula da harkokin jin dadin al'umma Amira Elfadil, ta ce kamata ya yi kasashe mambobin kungiyar ta AU, su amince da kundin, kamar yadda yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta nahiyar ko AfCFTA ta tanada. Ta ce, kaurar jama'a barkatai daga wasu sassan nahiyar zuwa sauran yankuna na duniya, da karuwar masu gujewa muhallan su, na zama wani babban kalubale ga kasashen Afirka.
Kasashe 33 ne dai suka sanya hannu kan yarjejeniyar ta AfCFTA, kana 4 daga ciki suka mikawa AU takardun nuna cikakkiyar amincewa da ita. Wadannan kasashe dai su ne Rwanda, da jamhuriyar Nijar, da Mali da kuma Sao Tome da Principe.
Bisa tsarin yarjejeniyar, sai kasashe a kalla 15 sun tabbatar da amincewar su da ita kafin ta fara aiki gadan gadan. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China