Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yi kira da a dauki kwararan matakan magance manyan matsalolin lafiyar jama'a a Afirka
2019-11-07 09:38:03        cri

Kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta yi kira ga kasashen nahiyar, da ma hukumomi dake karkashin kungiyar, da su kara sa kaimi wajen ganin sun magance abubuwan dake ci gaba da zama barazana ga lafiyar al'ummar nahiyar.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin taron manyan jami'an nahiyar game da kiwon lafiyar jama'a, tana mai cewa, tsarin kiwon lafiyar jama'a a Afirka, yana inganta cikin sauri, amma kuma cututtuka na zama babbar barazana. A don haka ta jaddada bukatar kara himma a kokarin da ake yi na magance matsalolin dake barazana ga tsarin kiwon lafiya, da ma rayuwar al'ummomin naniyar.

Bugu da kari, kungiyar ta jaddada cewa, wajibi ne a kare lafiyar al'ummomin nahiyar daga barazanar cututtuka, musamman ta hanyar aiwatar da dokokin kiwon lafiya na kasa da kasa da sauran manufofin kungiyar da suka shafi batutuwan kiwon lafiya a nahiyar baki daya.

Cibiyar dakile da hana yaduwar cututtuka ta Afirka (Africa CDC), hukumar da majalisar gudanarwar AU ta kafa da nufin taimakawa kokarin kasashen Afirka a fannin kiwon lafiyar al'umma ce ta shirya taron.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China