2019-10-11 10:46:55 cri |
A yayin ganawar tasu, Liu He ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan yin shawarwari da kasar Amurka kan batun daidaituwar ciniki da wasu harkokin dake jan hankulan kasashen biyu, domin cimma sakamako mai gamsarwa. A nasu bangare kuma, Craig Allen da Myron Brilliant sun bayyana fatansu na samu ci gaba a shawarwari na wannan zagaye, yayin kara fahimtar juna tsakanin kasashen biyu, don share fagen shawarwarin da za a gudanar a zagaye na gaba, ta yadda za a gano baki zaren warware sabanin dake tsakaninsu da kuma dakatar da takaddamar ciniki dake tsakanin kasashen biyu.
Cikin ganawarsa da Kristalina Georgieva, Liu He ya bayyana cewa, kasar Sin tana son cimma ra'ayi daya da kasar Amurka kan wasu batutuwan da suka dauki hankalin kasashen biyu bisa ka'idar mutunta juna da adalci, domin hana karuwar sabanin dake tsakaninsu. A nata bangare kuma, malama Georgieva ta ce, Asusun IMF yana yabawa matuka da kokarin da Sin ta yi wajen warware sabanin dake tsakaninta da Amurka ta hanyar yin shawarwari, kuma yana son ba da gudummawa yadda ya kamata kan harkokin kiyaye tsarin cinikin dake tsakanin bangarori daban daban da kuma kare ka'idojin ciniki cikin 'yanci. (Maryam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China