![]() |
|
2019-10-17 10:48:29 cri |
Tsawon titin zai kai kilomita 26.8, saurin tafiyar motoci kan wannan titin zai kai kilomita 80 cikin awa daya. Hanyar ta kuma bi ta filin jiragen sama na kasa da kasa na Jomo Kenyatta da kuma cibiyar kasuwanci ta birnin Nairobi da sauran yankuna, gaba daya an zuba jari na dalar Amurka miliyan dari 6 domin aikin gina wannan hanya.
A yayin bikin, shugaba Kenyatta ya bayyana cewa, gina babbar hanyar motar zai taimakawa kasar Kenya wajen raya ababen more rayuwar kasar. Kana, bisa labarin da aka samu an ce, hanyar da za a gina din zata rage cunkoson motoci a cibiyar birnin Nairobi, tare da rage kudaden tafiyar da motoci a kan hanya, lamarin da zai rage sa'o'i biyu da ake batawa a sanadiyyar cunkoson ababen hawa akan hanyar a lokutan safiya da yammaci.
Haka kuma, za a samar da guraben aikin yi kimanin dubu 3 a lokacin da ake aikin gina wannan hanya, yayin da za'a samar da guraben aikin yi 500 a lokacin da ake amfani da hanyar. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China