Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya ta kaddamar da gangamin karfafa neman kujera a kwamitin sulhu na MDD
2019-09-14 16:21:58        cri
Kasar Kenya ta kaddamar da gangamin karfafa damarmakinta na samun kujera a kwamitin sulhu na MDD, yayin zaben da za a yi a watan Yunin badi.

Manyan jami'an Kenya, sun ce gangamin zai bayyana irin kimar Kenya a matsayin mai tsayawa ga tabbatar da zaman lafiya da tsaro da ci gaba a yankin gabashin Afrika da sauran sassa.

Sakatariyar ma'aikatar harkokin wajen kasar Monica Juma, ta ce gangamin na neman kujerar, zai dogara ne kan karfin kasar na warware rikici da samar da tsaro da ci gaba.

Ta ce Kenya ta samu goyon baya mai karfi a kokarin da take na samun kujera a hukumar MDD mafi muhimmanci dake yanke muhimman shawarwari kan batutuwan tsaro da zaman lafiya a duniya.

Ta kara da cewa, baya ga goyon bayan da Tarayyar Afrika ta ba takarar kasar, ta na ci gaba da samun goyon baya daga nahiyoyin Asiya da Turai da Amurka.

Ana sa ran kenya za ta bi sahun takwarorinta na Afrika da suka hada da Tunisia da Niger, da aka zaba a watan Yuni, wajen samun kujerar wucin gadi a kwamitin sulhun. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China