Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sinawa yan yawon bude ido miliyan 782 ne suka yi bulaguro a lokacin hutun ranar kafuwar kasa
2019-10-08 10:30:26        cri

Ma'aikatar raya al'adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta sanar da cewa Sinawa masu yawon bude ido na cikin gida miliyan 782 ne suka yi tafiye tafiye a lokacin hutu kwanaki 7 na bikin murnar kafuwar kasa, adadin da ya karu da kashi 7.81 bisa 100 a makamancin lokacin bara.

A cewar ma'aikatar, adadin kudaden shigar da Sin ta samu a fannin yawon shakatawa ya tasamma yuan biliyan 650 kwatankwacin dala biliyan 90.94 daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Oktoba, adadin da ya karu da kashi 8.47 bisa 100 a makamancin lokacin bara.

Sama da tafiye tafiye miliyan 7 Sinawa suka yi zuwa kasashen ketare a lokacin hutun, a cewar ma'aikatar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China