Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Sin da Guinea sun aikawa wa juna sakon murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu
2019-10-04 16:18:37        cri

A yau Jumma'a 4 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Guinea Alpha Condé suka aikawa juna sako, domin murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

A cikin sakonsa, shugaba Xi ya nuna cewa, Guinea ita ce kasa ta farko a yankin kudu da hamadar Sahara, wadda ta kulla huldar diplomasiyya tare da kasar Sin. A cikin shekaru 60 da suka gabata, duk da sauye-sauyen da ake fuskanta a duniya, ko da yaushe bangarorin biyu suna nuna wa juna sahihanci da aminci, da ma mara wa juna baya, lamarin da ya sa dangantakarsu ta zama abin koyi a hadin kan Sin da Afirka. Shugaba Xi ya kara cewa, yana son hada kai tare da shugaba Conde, da kuma yin amfani da damar raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" da ma ci gaban hadin kan Sin da Afirka, wajen inganta zumuncinsu da kyautata hadin gwiwarsu, bisa aniyar ciyar da dangantakar abuta ta hadin kansu bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni zuwa gaba.

A nasa bangare, shugaba Conde ya bayyana cewa, kasashen biyu sun dade suna kiyaye huldar abota ta musamman, wadda ta shaida hadin gwiwar aminci a tsakanin Sin da Afirka. Bangaren Guinea ya jinjina shawarar "ziri daya da hanya daya", kuma yana son hada kai tare da Sin wajen aiwatar da sakamakon da aka samu a yayin taron koli na Beijing na dandalin FOCAC, a kokarin inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China