Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin ya yi kira da a taimakawa ci gaban matasan Afirka
2019-10-03 15:02:23        cri

Wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana cewa, muddin ana son a samar da zaman lafiya da tsaro da ci gaba a nahiyar Afirka, wajibi ne a goyi baya da ma kula da ci gaban matasan dake nahiyar.

Zhang Jun ya bayyana hakan ne yayin zaman muhawarar kwamitin tsaron MDD kan zaman lafiya da tsaro a Afirka. Yana mai cewa, akwai tarin matasa a nahiyar Afirka, a hannu guda kuma matasan sun shiga ayyukan gina kasa yadda ya kamata, sun kuma taka muhimmiyar rawa wajen farfado da nahiyar.

Sai dai kuma, tashe-tashen hankulan kungiyoyin masu dauke da makamai da rashin ci gaba, sun shafi matasan, haka kuma an mayar da su saniyar ware baya ga manyan kalubale kamar talauci da rashin aikin yi dake shafarsu.

A cewarsa, kasar Sin ta yanke shawarar hada kai da nahiyar Afirka don kafa cibiyoyin koyon sana'o'i na Luban guda 10 a sassan nahiyar, don horas da matasan Afirka dabarun koyon sana'o'i, kuma tuni aka kafa tare da bude cibiya ta farko a kasar Djibouti.

Ya ce, kasar Sin za ta samar da guraben karo ilimi 50,000 ga nahiyar Afirka, da damammaki na samun horo 50,000, inda za su halarci tarukan karawa juna sani. Haka kuma kasar Sin za ta gayyaci matasan Afirka 2,000 karkashin wani shiri na musayar ziyara.(Ibahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China