Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su tallafawa Afirka wajen cin gajiyar albarkatunta yadda ya kamata
2019-05-30 09:42:16        cri

Shugaban ofishin tsare tsaren siyasa na Sin a ofishin din din din na MDD Yao Shaojun, ya ce kasarsa na fatan gamayyar kasa da kasa za su tallafawa kasashen nahiyar Afirka, wajen cin cikakkiyar gajiyar albarkatunsu, tare da kawar da matsalar hakar ma'adanai, da cinikayyar su ba bisa ka'ida ba.

Yao ya yi wannan tsokaci ne yayin taron mambobin kwamitin wucin gadi, na kandagarkin tashe tashen hankula da warware rikici a nahiyar Afrika karkashin kwamitin tsaron MDDr.

Jami'in ya kara da cewa, ya kamata a hade sassan dokoki da na gudanarwa, da bangaren jami'an tabbatar da doka da na gwamnatoci, yayin da ake kula da ayyukan hakar ma'adanai, a kuma kara azama wajen kawar da ayyukan da suka sabawa doka na safarar su, tare da daukar matakan rage bukatar su a kasuwannin bayan fage.

Kaza lika a cewar sa, ya kamata MDD ta karfafa hadin gwiwa da kungiyar hadin kan kasashen nahiyar ta AU, da sauran kungiyoyin shiyya shiyya dake cikin ta, wajen ba da kariya ga albarkatu, da kuma dakile hakar su ba bisa ka'ida ba.

Jami'in ya ce, har kullum, Sin na bin akidar samar da daidaito, da cin gajiyar juna, da samun nasara cikin hadin gwiwa, tare da tallafawa sauran kasashe a fannin bunkasa ci gaban su yadda ya kamata. Har ila yau Sin na da burin ganin kasashen duniya sun lura da albarkatun su yadda ya dace, tana kuma adawa da hakar ma'adanai, da cinikayyar su ba bisa ka'ida ba.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China