Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabon sashen tashi da saukar jiragen sama na filin jirage dake Shanghai na daf da fara aiki
2019-09-10 10:47:38        cri

Sabon sashen tashi da saukar jiragen sama mafi girma, kuma irinsa na farko a duniya da aka gina, daura da filin jiragen sama na kasa da kasa dake birnin Shanghai na daf da fara aiki.

Mahukuntan filin jirgin saman na Shanghai Pudong, sun ce ana sa ran kaddamar da aikin wannan sashe ne tun daga ranar 16 ga watan nan na Satumba.

Sashen wanda yake bangaren kudu da sashe na daya da na biyu na filin jirgin, na da fadin sakwaya mita 622,000, kuma bangare ne na uku na aikin fadada filin jirgin saman, mai kunshe da wurin tashi, da na sauka, da na sauya jirage ga fasinjoji. Kaza lika an tanadi tsarin sufuri mai matukar sauri dake iya kai fasinjoji tsohon sashen filin jirgin cikin mintuna biyu da rabi, wanda shi ne irinsa mafi sauri da za a yi amfani da shi.

Kasancewar filin jirgin na da sassan zirga-zirgar fasinjoji 4, da na dakon kayayyaki 5, da wuraren tashin jirage 6, a shekarar bara yawan fasinjojin da suka yi zirga-zirga ta filin jirgin sun kai miliyan 118, wanda hakan ya sanya shi zama a matsayi na 4 a duniya cikin shekaru 3 a jere.

A hannu guda kuma, kididdiga ta nuna cewa, yawan kayayyaki da aka yi safarar su ta filin jirgin na Shanghai Pudong, sun kai tan miliyan 4.18, wanda hakan ya sanya ya zamo na 3 cikin shekaru 11 a jere.

Mahukuntan birnin Shanghai dai na fatan mayar da birnin wata cibiyar sufuri ta kasa da kasa mafi kasaita, wadda za ta hade dukkanin sassa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China