2019-06-26 11:17:49 cri |
A yayin ganawar, Wang Yi ya bayyana cewa, yayin da kasar Sin ke mu'amala da kasashen Afirka, tana mara musu baya wajen kare ikon mallakar kasa da tabbatar da zaman lafiya gami da neman ci gaba. Haka kuma Sin na nuna goyon-baya ga kasashen Afirka wajen kara taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, tare kuma da kare hakkokin kasashen Sin da Afirka da na sauran wasu kasashen dake tasowa.
Wang ya ce, makasudin shirya taron tabbatar da sakamakon da aka cimma a taron kolin FOCAC, wato dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka shi ne, kara tuntubar juna tsakanin Sin da Afirka da cimma daidaito da kara dankon zumunci tsakaninsu.
A ranar kuma, memba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Yang Jiechi ya gana da wasu ministocin harkokin waje na kasashen Afirka, ciki har da na Saliyo da Equatorial Guinea da Afirka ta Kudu da Senegal.(Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China