Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin PowerChina ya horas da kwararrun Zambiya kusan dari uku a fannin samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa
2019-09-17 14:08:53        cri
Rahotanni daga babban kamfanin kula da ayyukan samar da wutar lantarki mai suna PowerChina na kasar Sin sun ce, kwalejin horas da fasahar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa da kamfanin ya bada tallafin ginawa, ya fara daukar dalibai a fadin Zambiya. A halin yanzu kwalejin ya horas da dalibai 289 gaba daya. Kwalejin mai fadin murabba'in mita 2813 ya kunshi ajujuwa 4, wadda ke da fannonin koyarwa guda shida, ciki har da gyara motoci da gwaje-gwaje da kuma gine-gine da sauransu.

Kwalejin horas da ma'aikata masu fasaha kyauta a Zambiya, yana kuma biyan bukatun kafa tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa. A ranar 18 ga watan Yulin shekara ta 2017 ne, shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu ya kaddamar da kwalejin, wadda ke ci gaba da horas da ma'aikatan wurin a halin yanzu. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China