2019-06-04 09:42:13 cri |
Davies Mwila, sakatare-janar na jam'iyyar Patriotic Front (PF), ya bayyana hakan a lokacin gudanar da taron kwamitin tsakiya na kolin jam'iyyar a ranar 2 ga watan Yuni, da nufin lalibo bakin zaren magance matsalar kalaman batanci da magoya bayan jam'iyyu ke aikatawa.
Ya ce kirkiro kwamitin sanya ido game da shafukan sada zumuntan zai taimaka wajen yaki da masu aikata laifin kalaman batanci ta kafafen sada zumuntar, kuma ba za'a laminci duk wani batu da ya shafi cin mutunci ko cin zarafi a jam'iyyar ba.
Tuni dai hukumar kolin jam'iyyar ta umarci dukkan shugabannin larduna da su dinga tuntubar babbar sakatariyar jam'iyyar ta kasa domin su sanya ido tare da yin rejistar dukkan shafukan sada zumunta da aka kirkira a matakan gundumomi da na larduna. (Ahmad Fagam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China