2019-09-06 09:23:53 cri |
A yayin ganawar, Yang Jiechi ya bayyana cewa, akwai kyakkyawar makoma kan bunkasuwar kasashen Sin da Nijeriya. Ya kamata Sin da Nijeriya su kara yin mu'amala a tsakanin manyan jami'ansu, da inganta hadin gwiwarsu a harkokin kasa da kasa da yankuna. Ya ce, an samu nasarori a hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni daban daban, wadanda suka amfanawa kasashen biyu da jama'arsu. Sin ta bukaci karin kamfanonin kasar da su zuba jari a kasar Nijeriya. Yang ya kara da cewa, ya kamata a ci gaba da yin kokarin raya shawarar "ziri daya da hanya daya", da aiwatar da ayyukan da aka cimma a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka don zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da Nijeriya.
A nasa bangare, shugaba Buhari ya bayyana cewa, kasarsa tana maraba da karin kamfanonin Sin da su zuba jari a kasar. Ya ce, Nijeriya ta nuna yabo ga shawarar "ziri daya da hanya daya", kuma tana fatan hada kai tare da kasar Sin wajen aiwatar da sakamakon da aka cimma a gun taron kolin Beijing na FOCAC, ta yadda za a inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China