2019-05-17 11:06:21 cri |
Zhou Pingjian, jakadan kasar Sin a Nijeriya ya bayyana a yayin taron cewa, kasar Sin tana son inganta tuntuba da cudanya da Nijeriya, da zurfafa dankon zumunci a tsakanin jama'ar kasashen 2 da kyautata hadin gwiwarsu ta fuskar tsaro, da kara azama kan aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", a kokarin kara kawo wa kasashen 2 da jama'arsu alheri na a-zo-a-gani.
Mahalarta taron 'yan Nijeriya, sun yi kira ga gwamnatin kasar da ma bangarori daban daban na kasar, da su yi koyi da kyawawan fasahohin kasar Sin wajen farfado da kasa da fitar da jama'a daga talauci. Suna ganin cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya", ba shawarar yin hadin gwiwa ba ne kadai ga Nijeriya, domin za ta sabunta huldar abota a tsakaninta da sauran kasashe. Sun ce kamata ya yi Nijeriya ta bude kofarta ga shawarar ba tare da wata rufa-rufa ba, ta kuma yi amfani da damar da shawarar za ta kawo mata domin gaggauta raya kanta. (Tasallah Yuan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China