Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta dauki matakan daidaita bunkasar tattalin arzikinta
2019-09-05 11:23:02        cri

Majalisar gudanarwar kasar Sin, ta yi kira da a kara zage damtse, wajen daukar matakan da za su taimakawa kasar daidaita muhimman alkaluman tattalin arzikin da take fatan cimmawa.

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, wanda ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa da aka fitar bayan kammala taron majalisar gudanarwar kasar da ya jagoranta, ya ce za a kara daukar matakai, don daidaita yadda ake samar da ayyukan yi, da bangaren harkokin kudi, cinikayyar ketare, da jarin cikin gida da na waje, da ma hasashen da ake da shi a ragowar sassa.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, bunkasuwar tattalin arzikin kasar, ya daidaita, har ya kara bunkasa a watanni shida na farkon bana.

Sanarwar ta kara da cewa, sakamakon sarkakkiya da kalubale daga waje, ya sa tattalin arzikin kasar na fuskantar karin matsin lamba. Don haka, ya kamata a kara mayar da hankali wajen daukar matakai da manufofin da suka dace na tabbatar da bunkasar tattalin arzikin.

A hannu guda kuma, gwamnati na duba yiwuwar kara daukar dalibai a kwalejoji da makarantun koyar da sana'o'i da ma samar da tallafin kudaden koyar da sana'o'i.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China