Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta kasance jigon ci gaban tattalin arzikin duniya cikin shekaru 70 da suka gabata
2019-08-30 10:12:29        cri

Kasar Sin kasa ce ta 1 a fanni bada gudunmuwa ga ci gaban tattalin arzikin duniya tun daga 2016, inda ta zama jigon dake ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya.

Rahoton da hukumar kididdiga ta kasar ta fitar, ta ce cikin shekaru 70 da suka gabata, gudumuwar kasar Sin ga ma'aunin muhimman bangarorin tattalin arziki da zaman takewa ta ci gaba da karuwa, haka zalika matsayinta da tasirinta a duniya, sun ci gaba da samun ingantuwa.

Rahoton ya nuna cewa daga shekarar 1961 zuwa 1978, matsakaiciyar gudunmuwar da kasar Sin ta bayar ga ci gaban tattalin arzikin duniya a kowacce shekara ya tsaya ne kan kashi 1.1. Amma daga 1979 zuwa 2012, adadin ya karu zuwa kaso 15.9, lamarin da ya kai ta matsayi na biyu a duniya a wannan fanni.

Daga shekarar 2013 zuwa 2018 kuwa, gudunmuwar da Kasar Sin ta ke ba tattalin arzikin duniya a kowacce shekara, ya tashi kaso 28.1, wanda ya kai ta matsayi na 1 a duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China