2019-09-05 10:30:10 cri |
Wata kungiyar kwararru ta kasar Zambiya ta ce, ci gaban da kasar Sin ta samu a cikin shekaru 70 da suka gabata ya samar da muhimmin darasi ga kasashen Afrika wadanda ya kamata su dau izina.
Chenai Mukumba, mai sulhuntawa dake aiki a cibiyar kasa da kasa ta kungiyar masu sayayya (CUTS), ta ce babu shakka, ci gaban da kasar Sin ta samu a cikin shekaru 70 ya haifar da muhimmin sakamako, matakin da ya baiwa kasar damar zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Ta ce hakika, shugabannin kasar Sin sun yi kyakkyawan tanadi na ganin kasar ta samu nasarori a cikin shekaru 70 din da suka gabata, ya kamata mu koyi darasi game da yadda wannan shiri ya kai ga nasara.
Ta kara da cewa, a halin yanzu kasar Sin ta fita zuwa kasashen ketare inda ta zuba jari a sauran kasashen duniya, kuma ta zuba jari mai dunbun yawa a fannin ayyukan gina kayayyakin more rayuwa, musamma a kasashen Afrika.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China