Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta gina makamashin nukiliya marar hadari
2019-09-05 10:13:21        cri

Jami'in ma'aikatar kiyaye muhallin kasar Sin ya sanar cewa, kasar za ta samar da makamashin nukiliya wanda ba shi da hadari ko kadan.

Liu Hua, mataimakin ministan ma'aikatar kare muhalli da gandun daji (MEE), kuma daraktan tsaron makamashin nukilya na kasar Sin, ya bayyanawa manema labarai cewa, tsarin sanya ido da gudanarwar nukiliyar kasar Sin a fili ne ake karara, kuma ya samu amincewar hukumomin kasa da kasa.

Cikin wata takardar bayani da aka fitar a ranar Talata, mai taken "tsaron nukiliya a kasar Sin", an ce daga cikin jerin kasashen duniya da suke sahun gaba ta fuskar ingantaccen tsarin tafiyar da makamashin nukiliya, kasar Sin ta jima da kafa tarihi wajen kulawa da kuma ingancin nukiliyarta. Takardar bayanin ta ce, kasar Sin za ta ci gaba da amfani da fasahar nukiliya mai inganci, tsarin kula da kayayyakin nukiliyarta yana da karfi, kuma ana ci gaba da kokarin tabbatar da lafiyar al'umma da muhalli.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China