Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin kasar Sin: Mutunta juna shi ne tushen tabbatar da tsaron nukiliya
2019-05-23 11:16:52        cri

Jakadan kasar Sin mai kula da harkokin kwance damarar makamai, Li Song ya bayyana cewa, muddin kasashen duniya ba sa mutunta juna da ma harkokinsu na tsaro, sannan ba a kokarin tabbatar da tsaro na bai daya, batun tsaron nukiliya magana ce ta fatar baka kuma shirme ne kawai. Ko kuma wani makami ne na mai karfi da ya ci zalin maras karfi.

Li Song ya fadawa zaman taron kwance damara da ya gudana a birnin Geneva jiya Laraba cewa, yin komai a bayyane hanya ce ta tabbatar da mutunta juna da kaucewa bahuguwar fahimta da rage tankiya.

Da yake mayar da martani kan zargin baya-bayan nan da wani babban jami'in Amurka ya yi cewa, Kasar Sin tana yin rufa-rufa game da shirinta na zamanatar da nukiliya wanda ya haifar da tambayoyi kan aniyyarta kan wannan batu a nan gaba. Li ya bayyana cewa, wannan na daga cikin misalin da wasu ke fakewa da su suna nuna yatsa kan wasu.

Jami'in na kasar Sin ya ce, Amurka ta sha fadan cewa, wasu kasashe na sanya mata damuwa kan tsaronta. Ya ce, duk kasar da ke daukar sauran kasashe a matsayin abokan gabanta, da alamun za ta kara samun abokan gaba, duk da cewa, ba haka ne a cikin zukatansu ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China